News RSS/Atom Viewer Classic
Sponsored Links
A Nigeria an samu nasarar shawo kan gobarar da ta tashi a kasuwar kantin kwari dake jahar Kano a arewacin kasar. Kungiyar Red Cross ta ce mutane biyu ne suka rasa rayikansu.
Shugaban mulkin sojin Nijer, Manjo Salou Djibo ya sa hannu kan wata dokar da ta haramtawa sojoji da ministoci gwamnatin riko shiga zabubuka masu zuwa.
Mukaddashin shugaban Nigeria ya kafa wani kwamiti da zai binciki sayar da kamfanin sadarwar nan na kasa, NITEL da aka yi a watan jiya.
Bayan an shafe tsawon lokaci ana ta jayayya yanzu haka an cimma matsaya akan yadda za'a biya diyya ga wadanda harin da kaiwa cibiyar kasuwanci ta birnin New York ya shafa.
'Yan sanda a Pakistan sun ce, 'yan kunar bakin-wake sun tada wasu bama-bamai biyu a birnin Lahore, inda suka hallaka mutane arba'in da biyar.
A jamhuriyar Nijar, hukumomin sojin kasar sun jaddada soke sammacin kama wasu gaggan 'yan siyasar kasar da tsohuwar gwamnatinn Tanja ta nemi kamawa.
Rundunar sojan Najeriya ta karyata zarge-zargen da jami'an gwamnatin jahar Plateau suka yi, cewa ta yi biris da gargadin da aka yi na shirin kai hari wasu kauyuka.
A Nigeria, kungiyar Miyatti Allah ta bayyana takaicinta dangane da abin da ta kira, shafawa Fulani kashin kaji a kan hare-haren baya-bayan nan a jihar Filato.
Masu fafutuka a jamhuriyar dimokradiyyar Congo sun ce tsoffin 'yan tawayen kasar na cigaba da zaluntar masu hakar ma'adinai.
Sabon jadawalin sunayen mutanen da suka fi kudi a duniya ya tabbatar da cewa China ce tafi kowace kasa yawan biloniyoyi in banda Amurka.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna cewa kusan rabin agajin abinci, da ake kaiwa Somalia ana karkatar da shi ne.
A Nijar kungiyar 'yan kasuwa na Yamai ta dau matakin rage farashin kayan abinci, a matsayin gudunmawa ga shirin gwamnati na samar da cimaka ga masu fuskantar yunwa.
Gwamnatin Najeriya na cigaba da shan matsin lamba daga kasashen duniya dangane da kashe-kashen da aka yi na baya-bayan bayan nan a daura da garin Jos.
Hukumomi da kungiyoyi suna matsin lamba ga gwamnatin Nijeriya ta gudanar da cikakken bincike a kan hare hare na baya bayan nan a jihar Filato.
Duk da cewa dai hukumar kula da muhalli a Abuja ta tsara yadda jama'a za su rika fito da shara, da kuma kwashe ta domin tsaftace birnin, har yanzu shara na ci gaba da dabaibaye manyan titunan birnin.
Lars Lagerback ya shiga harkar kwallon kafa ne dumu dumu a shekarar alif dari tara da saba'in da bakwai inda ya bugawa tawagar kasar Sweden kwallo.
Kauyen 'Zimbabwe' dake karamar hukumar Karshi ta jihar Nasarawa a Najerira wani kauye ne da jama'a da dama ke zuwa domin shakatawa.
Rudunar 'yan sadan Jihar Filato ta ce za ta gurfanar da mutane arba'in da tara ne a gaban kotun, da tuhumar su da kisa a rikicin da ya barke kwana kwana nan a rikicin Jos.
Hukumomi da kungiyoyi suna matsin lamba ga gwamnatin Nijeriya ta gudanar da cikakken bincike a kan hare hare na baya bayan nan a jihar Filato.
Sabon rikici ya sake barkewa a Dogo Nahawa, 'yan kilomitoci kadan daga cikin garin Jos da ke jihar Filato a ranar Lahadi 7 Maris 2010, bayan rikicin watan Janairu.
A Najeriya koma bayan da karancin wutar lantarki ke haifarwa a bangaren masana'antu da ci gaban kasar.
Alkalluma sun nuna cewar kashi saba'in cikin dari na Yan Najeriya manoma ne, amma saboda rashin samun kyakkyawar yabanya, su kansu, ba sa koshi.
Duk da irin korafin da jama'a ke yi sakamakon takurar da suke samun kansu a ciki saboda tsanantar zafi, ga wasu kuma lokaci ne na murna.
An kiyasta cewa mutane dari biyu sun halaka a rikicin da aka yi a Dogo-Nahawa, wanda kuma a cewar gwamnatin jihar , yawanci mata ne da yara kanana.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya ta nada Lars Lagerback a matsayin mai horad da 'yan wasan Super Eagles.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagwon kasa, wato EFFC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu a babbar kotun tarraya da ke Lafia babban birnin jihar Nasarawa a ranar Laraba 3 ga watan Maris.
A cikin wata Maris din shekarar 2009 ne Sashen Hausa na BBC ya gudanar da wani rangadi a jihohi goma sha daya na arewacin Najeriya. Rangadin ya mayar da hankali ne kan yadda rayuwa take a yankunan karkara.
Shirya gajeran fim kan yadda kake kallon duniya, ka aiko wa BBC don shiga gasa da kuma samun damar watsa wa ga duniya.
Sofomo ™ © 2007