Tsohon shugaban sojan kasar Sri Lanka, janar Sarath Fonseka mai ritaya na gurfana gaban kotun soji bisa zargin shiga siyasa alhali yana cikin kakin soja.
Rahotanni daga jahar Kano a arewacin Najeriya na cewa an samu barkewar cutar sankarau a wasu sassan jahar inda lamarin ya shafi kimanin kananan hukumomi 23.
Wasu bama-bamai guda biyu sun tashi a gidan gwamnatin jihar Delta da ke Warri gab da za a fara wani taron neman zaman lafiya. Kungiyar MEND ta bayyana cewa ita ce ke da alhakin dasa bama baman.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta`annati ta EFCC a Nigeria, ta ce ta fara gudanar da wani sabon bincike a kan tsohon Gwamnan jihar Delta, James Ibori.
A Nijeriya akalla mutane goma sha takwas ne suka mutu a wata taho-mu gama da aka yi tsakanin wata motar daukar kasa watau Tipa da wata motar fasinja a Katsina.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijer ya gaana da kungiyoyin farar hula da suka hada da kungiyoyin ma'aikata da kungiyoyin kare hakin dan Adam da na 'yan kasuwa.
Daya daga cikin fitattun yan kwallon duniya, David Beckham na kasar Ingila, ya ji rauni a lokacinda ya ke bugawa kulob dinsa na AC Milan kwallo a daren jiya.
Gwamnatin Amurka ta baiwa iyalan jami'anta da ke aiki a garuruwan da ke kan iyakarta da kasar Mexico izinin kauracewa yankin bayan jerin wasu hare hare.
Duk da cewa dai hukumar kula da muhalli a Abuja ta tsara yadda jama'a za su rika fito da shara, da kuma kwashe ta domin tsaftace birnin, har yanzu shara na ci gaba da dabaibaye manyan titunan birnin.
A Nijeriya, wata gobara da ta tashi a kasuwar kantin kwari dake jahar Kano a arewacin kasar, ta yi sanadiyyar konewar dubban shaguna da kuma asarar kaya na biliyoyin Nairori.
Rudunar 'yan sadan Jihar Filato ta ce za ta gurfanar da mutane arba'in da tara ne a gaban kotun, da tuhumar su da kisa a rikicin da ya barke kwana kwana nan a rikicin Jos.
A Nijeriya, wata gobara da ta tashi a kasuwar kantin kwari dake jahar Kano a arewacin kasar, ta yi sanadiyyar konewar dubban shaguna da kuma asarar kaya na biliyoyin Nairori.
A cikin wata Maris din shekarar 2009 ne Sashen Hausa na BBC ya gudanar da wani rangadi a jihohi goma sha daya na arewacin Najeriya. Rangadin ya mayar da hankali ne kan yadda rayuwa take a yankunan karkara.