Rundunar tsaro ta gamayya a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Nijeriya ta tabbatar da kai wani hari da ya lalata bututun mai dake garin Buguma a jihar Rivers.
A jamhuriyar Nijar shugaban mulkin sojan kasar Manjo Salou Djibou ya jagoranci wani taro da ya hada wakilan jami'an tsaro daban-daban akan majalisar tuntubar juna.
A jamhuriyar Nijar, wata kungiyar agaji ta ce da dama daga cikin mutane miliyan bakwai da rabi da matsalar karancin abinci ta shafa sun fara fuskantar yunwa.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jamiyyar ANPP Janarar Muhammadu Buhari mai ritaya ya bayyana shiga jamiyyar CPC, daya daga cikin jamiyyun kasar da aka yi mata rajista a baya bayan nan.
A Najeriya, jami'yyar PDP mai mulkin kasar ta ce ta yi na'am, da matakin da mukaddashin shugaban kasar mista Goodluck Jonathan ya dauka na rusa majalisar zartarwar kasar a yan kwanakin baya baya nan.
Gwamnatin Najeriya ta bukaci jakadanta na Libiya ya koma gida, a wani mataki na nuna bacin ranta da wasu kalaman da Shugaba Libiyar, Mu'ammar Gaddafi yayi a kwanan nan.
Kwamitin majalisar dattawan Najeriya kan gyaran fuska ga tsarin mulkin kasar, wadanda suka shafi dokokin zabe, ya mika rahotonsa na farko ga majalisar dattawan kasar.
Wasu bama-bamai guda biyu sun tashi a gidan gwamnatin jihar Delta da ke Warri gab da za a fara wani taron neman zaman lafiya. Kungiyar MEND ta bayyana cewa ita ce ke da alhakin dasa bama baman.
Duk da cewa dai hukumar kula da muhalli a Abuja ta tsara yadda jama'a za su rika fito da shara, da kuma kwashe ta domin tsaftace birnin, har yanzu shara na ci gaba da dabaibaye manyan titunan birnin.
A Nijeriya, wata gobara da ta tashi a kasuwar kantin kwari dake jahar Kano a arewacin kasar, ta yi sanadiyyar konewar dubban shaguna da kuma asarar kaya na biliyoyin Nairori.
Mai'katan tsaron Najeriya ta lallata wasu nakiyoyi guda dari da biyu da aka samu a yayin da ake aikin ginin hanya a garin Fatakwal dake kudu maso kudancin Kasar.
A cikin wata Maris din shekarar 2009 ne Sashen Hausa na BBC ya gudanar da wani rangadi a jihohi goma sha daya na arewacin Najeriya. Rangadin ya mayar da hankali ne kan yadda rayuwa take a yankunan karkara.