Sponsored Links
Sakatare Janar na MDD Ban Ki-Moon, ya isa gabas ta tsakiya, domin farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Israila da Falasdinawa
2010-03-20T06:55:55+00:00
Mahukunta na Falasdinawa sun ce jiragen yakin Israila sun kai hare hare a Gaza, a dare na ukku a jere. Sun ce an kai harin ne kan wani filin jirgin saman da ba a amfani da shi da kuma wani bututu.
2010-03-20T07:05:46+00:00
Dalibai a birnin Jos dake Najeriya, sun yi kokarin kashe mutum a jiya, wanda suke zargi da shiga da bam cikin dakunan kwanan su.Sojoji ne suka ceto mutumin, wanda baya dauke da wani bam ko makami.
2010-03-20T07:16:01+00:00
Yajin aikin kwanaki ukku da ma'aikatan dake hidima a cikin jiragen sama, ya fara gurgunta harkokin daya daga cikin kamfanonin jiragen sama na duniya mafi karfi, wato British Airways.
2010-03-20T07:24:21+00:00
Shugaban Amuka Barack Obama ya kara bayyana dalilan da suka sa yake son aiwatar da sauye sauye kan harkokin kiwon lafiya a wani gangami a Amurka.
2010-03-19T20:50:21+00:00
Rundunar tsaro ta gamayya a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Nijeriya ta tabbatar da kai wani hari da ya lalata bututun mai dake garin Buguma a jihar Rivers.
2010-03-19T20:54:14+00:00
A jamhuriyar Nijar shugaban mulkin sojan kasar Manjo Salou Djibou ya jagoranci wani taro da ya hada wakilan jami'an tsaro daban-daban akan majalisar tuntubar juna.
2010-03-19T20:47:04+00:00
Babban magatakardan majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon, ya yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da shirinta na gina matsugunnan Yahudawa.
2010-03-19T15:10:42+00:00
A jamhuriyar Nijar, wata kungiyar agaji ta ce da dama daga cikin mutane miliyan bakwai da rabi da matsalar karancin abinci ta shafa sun fara fuskantar yunwa.
2010-03-19T15:57:17+00:00
Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jamiyyar ANPP Janarar Muhammadu Buhari mai ritaya ya bayyana shiga jamiyyar CPC, daya daga cikin jamiyyun kasar da aka yi mata rajista a baya bayan nan.
2010-03-19T07:48:00+00:00
A Najeriya, jami'yyar PDP mai mulkin kasar ta ce ta yi na'am, da matakin da mukaddashin shugaban kasar mista Goodluck Jonathan ya dauka na rusa majalisar zartarwar kasar a yan kwanakin baya baya nan.
2010-03-19T07:54:23+00:00
Gwamnatin Najeriya ta bukaci jakadanta na Libiya ya koma gida, a wani mataki na nuna bacin ranta da wasu kalaman da Shugaba Libiyar, Mu'ammar Gaddafi yayi a kwanan nan.
2010-03-18T20:13:52+00:00
Wasu bama-bamai guda biyu sun tashi a gidan gwamnatin jihar Delta da ke Warri gab da za a fara wani taron neman zaman lafiya. Kungiyar MEND ta bayyana cewa ita ce ke da alhakin dasa bama baman.
Hukumomi da kungiyoyi suna matsin lamba ga gwamnatin Nijeriya ta gudanar da cikakken bincike a kan hare hare na baya bayan nan a jihar Filato.
Duk da cewa dai hukumar kula da muhalli a Abuja ta tsara yadda jama'a za su rika fito da shara, da kuma kwashe ta domin tsaftace birnin, har yanzu shara na ci gaba da dabaibaye manyan titunan birnin.
Lars Lagerback ya shiga harkar kwallon kafa ne dumu dumu a shekarar alif dari tara da saba'in da bakwai inda ya bugawa tawagar kasar Sweden kwallo.
Fasahar intanet fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duk fadin duniya.
A Nigeria, rushe majalisar zartarwa da mukaddashin shugaban kasar Goodluck Jonathan yayi, na ci gaba da haifar da cece kuce.
Wani dattijo mai shekaru tamanin da takwas Alhaji Garba Magini ya yanke shawarar shiga makarantar firamare domin nunawa 'yan baya mahimmancin ilimi.
2010-03-15T13:58:24+00:00
A Nijeriya, wata gobara da ta tashi a kasuwar kantin kwari dake jahar Kano a arewacin kasar, ta yi sanadiyyar konewar dubban shaguna da kuma asarar kaya na biliyoyin Nairori.
Mai'katan tsaron Najeriya ta lallata wasu nakiyoyi guda dari da biyu da aka samu a yayin da ake aikin ginin hanya a garin Fatakwal dake kudu maso kudancin Kasar.
Fasahar intanet fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duk fadin duniya.
Gwamnatin jihar Kaduna dai na ikirarin inganta hakar ilimin Firamare a Jihar, bayan da ake samun irin wadannan makaratu
A cikin wata Maris din shekarar 2009 ne Sashen Hausa na BBC ya gudanar da wani rangadi a jihohi goma sha daya na arewacin Najeriya. Rangadin ya mayar da hankali ne kan yadda rayuwa take a yankunan karkara.
Shirya gajeran fim kan yadda kake kallon duniya, ka aiko wa BBC don shiga gasa da kuma samun damar watsa wa ga duniya.
2010-02-08T21:00:57+00:00
Sofomo ™ © 2007